Posts

Showing posts from March, 2026

KYA Ta Jinjinawa W.O. Idris Abdullahi (Idi Soja Kauru) Bisa Gudummawar Da Yake Bayarwa Ga Al’ummar Kauru.

Image
A kowace al’umma akwai wasu mutane da ayyukansu na alheri ke sauya rayuwar jama’a. Daya daga cikin irin wadannan mutane a Karamar Hukumar Kauru shi ne Warrant Officer Idris Abdullahi, wanda aka fi sani da Idi Soja Kauru. Duk da cewa ba dan siyasa ba ne, amma ya dade yana nuna jajircewa wajen taimakawa al’ummarsa da inganta rayuwar jama’a. Daya daga cikin manyan gudummawar da Idi Soja ya bayar shi ne taimakawa matasan Kauru wajen samun ayyukan yi. Ta hanyar damar da ya samu da kuma kokarinsa, kamar yadda majiyarmu Ibrahim Jasing Kauru ya bayyana, ya taimaka wa wasu matasa da dama wajen samun aiki a hukumomin tsaro kamar ‘yan sanda, Fire Service da kuma rundunar sojojin kasa. A wannan lokaci da rashin aikin yi ke damun matasa da dama, irin wannan taimako ya bude sabbin hanyoyi na rayuwa ga iyalai da dama a Kauru. Baya ga wannan, Idi Soja yana yawan nuna tausayi da kulawa ga marasa karfi a cikin al’umma. Ya kasance yana taimakawa zawarawa, marasa lafiya da kuma iyalan da suka rasa masu t...