KYA Ta Jinjinawa W.O. Idris Abdullahi (Idi Soja Kauru) Bisa Gudummawar Da Yake Bayarwa Ga Al’ummar Kauru.


A kowace al’umma akwai wasu mutane da ayyukansu na alheri ke sauya rayuwar jama’a. Daya daga cikin irin wadannan mutane a Karamar Hukumar Kauru shi ne Warrant Officer Idris Abdullahi, wanda aka fi sani da Idi Soja Kauru. Duk da cewa ba dan siyasa ba ne, amma ya dade yana nuna jajircewa wajen taimakawa al’ummarsa da inganta rayuwar jama’a.

Daya daga cikin manyan gudummawar da Idi Soja ya bayar shi ne taimakawa matasan Kauru wajen samun ayyukan yi. Ta hanyar damar da ya samu da kuma kokarinsa, kamar yadda majiyarmu Ibrahim Jasing Kauru ya bayyana, ya taimaka wa wasu matasa da dama wajen samun aiki a hukumomin tsaro kamar ‘yan sanda, Fire Service da kuma rundunar sojojin kasa. A wannan lokaci da rashin aikin yi ke damun matasa da dama, irin wannan taimako ya bude sabbin hanyoyi na rayuwa ga iyalai da dama a Kauru.

Baya ga wannan, Idi Soja yana yawan nuna tausayi da kulawa ga marasa karfi a cikin al’umma. Ya kasance yana taimakawa zawarawa, marasa lafiya da kuma iyalan da suka rasa masu tallafa musu. Ayyukansa na alheri sun kai ga gidaje da dama a Kauru, musamman wadanda ke cikin mawuyacin hali.

Haka kuma, kulawarsa ga marayu abin yabawa ne matuka. Da yake fahimtar kalubalen da iyalan marayu ke fuskanta, ya tallafa wa gidaje da dama tare da taimakawa wasu yara marayu wajen ci gaba da karatunsu ta hanyar biyan kudin makaranta da samar musu da kayan karatu. Ta wannan hanya, yara da dama sun samu damar ci gaba da karatu cikin kwarin gwiwa da kwanciyar hankali.

A kwanakin nan ma, karamcinsa ya sake bayyana lokacin da ya bada tallafi ga wasu gidajen marayu a garuruwan Kadage da Kware. Wannan taimako ya kawo sauki ga iyalai da dama, har wasu daga cikin matan da aka tallafawa suka kasa boye farin cikinsu, suna ta yi masa addu’o’i na alheri.

Abin da ya fi daukar hankali a cikin ayyukan Idi Soja shi ne yadda yake yin wadannan ayyukan alheri ba tare da neman yabo ko wata riba ba. Abin da ke motsa shi shi ne tausayi, kishin al’umma da kuma burin ganin mutanen Kauru sun samu rayuwa mai inganci.

A matsayinmu na Kauru Youth Ambassadors (KYA), mun yi imanin cewa mutane irin su Idi Soja su ne ainihin misalin hidimar al’umma da jagoranci nagari. Ayyukansa sun nuna cewa sauyi na gaskiya ba lallai sai daga mukaman siyasa yake fitowa ba, yana iya fitowa daga zuciyar mutum mai son alheri ga jama’a.

Saboda haka, muna mika cikakkiyar godiya ga Warrant Officer Idris Abdullahi bisa irin gudummawar da yake bayarwa ga al’ummar Kauru. Taimakonsa ga matasa, marasa karfi da kuma marayu abin alfahari ne kuma abin koyi.

Haka kuma muna kira ga sauran masu hali da masu kishin al’umma, a cikin Kauru da wajen ta, da su yi koyi da wannan kyakkyawan misali. Al’ummarmu na bukatar karin mutane masu zuciya irin tasa, mutane da za su rika daga darajar wasu tare da taimakawa wajen cigaban al’umma. Muna addu’ar Allah Ya kara masa lafiya da karfin gwiwa, Ya kuma saka masa da alheri bisa dukkan ayyukan alherin da yake yi. 

Kauru Youth Ambassadors (KYA),
For Youth Advancement and Community Development.